Shekaru 32 da kisan dalibai a Nijar
February 9, 2022Daiban dai sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne, domin neman inganta dimukuradiyya da harkar ilimi a kasar. Zanga-zangar ta bana da ke zama karo na 32 kan kisan gillar daliban uku da dubban daliban jami'ar birnin Yamai din suka gudanar, ta wakana cikin kwanciyar hankali da lumana. Daliban jami'ar da ma na makarantun sakandaren birnin na yin jerin gwano daga cikin jami'ar zuwa tsakiyar babbar gadar birnin, inda a nan ne jami'an tsaron suka bindige daliban masu zanga-zangar neman kafa dimukuradiyya a kasar. Sai dai Marie chitou daya daga cikin daliban ta ce shekaru 32 bayan gwagwarmayar tasu, har yanzu dimukuradiyyar Nijar din na son gyara. Zanga-zangar shekara-shekarar ta daliban jami'ar Yamai din dai, na zaman zanga-zangar lumana mafi girma da ake shiryawa a kasar a kowace shekara. Daliban na share tsawon yini guda suna gabatar da makaloli kan ci-gaba ko akasin da aka samu a fannin dimukuradiyya da ma ingantuwar ilimi a kasar shekaru 32 bayan sadaukar da rayukan da 'yan uwansu uku suka yi.