OIC za ta taimaki 'yan Afghanistan
August 24, 2021A wani taron gaggawa da kungiyar ta gudanar a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, babban magatakardar kungiyar Dakta Yousef Bin Ahmad Bin Abdul Rahman Al-Othaimeen ya sanar da aniyar kungiyar na tura jakadu na musamman a wannan makon, domin jaddadawa sababbin shugabannin gwamnatin kasar muhimmancin zaman lafiya da sasanta juna gami da yin riko da matsakaicin ra'ayin addinin Islama da magabatan shugabanin Musulumci suka tafi a kansa. Kungiyar ta kara da yin kira ga 'yan Taliban din da su jagoranci tattaunawa da daukacin bangarorin kasar, domin shawo kan matsalolin da suka addabe al'umma baki daya.
A nasa bangaren, wakilin Saudiyya a taron, Dakta Saleh Hamad Al-Suhaibani ya nemi kasashen Musulmi da su bai wa 'yan kasar Afghanistan din duk wani taimakon da ya wajaba, domin ficewa daga cikin halin kangin da aka jefa su. 'Yan Taliban masu da'awar kishin Islama, sun fara mulkin Afghanistan tsakanin shekarun 1996 zuwa 2001. A wancan lokaic, sun bai wa shugaban kungiyar al-Qa'ida Osama bin Laden mafaka, wanda kungiyarsa ta dauki alhakin harin ranar 11 ga watan Satumban 2001 da aka kai a Amirka da ya yi sanadiyyar rasa rayuka 3,000. Kawancen kasashen yammacin Turai da Amirka na ci gaba da shan kakkausan suka dangane da janyewar da suka yi daga Afghanistan, abin da ya bai wa kungiyar Taliban damar sake kwace iko da kasar.