Ukraine:Olaf Scholz na Jamus zai gana da Macron don taimako
March 15, 2024A Jumma'ar nan ce shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron da firaministan Poland Donald Tusk, don lalubo hanyoyin samun hadin kan kasashen Turai bayan sabanin da suka samu kan tallafawa Ukraine, don ci gaba da kare kanta daga mamayar da Rasha ta yi mata.
Karin bayani:Zelensky zai halarci taron tsaro na Jamus
Tsohon ministan harkokin wajen Faransa kuma yanzu wakili na musamman ga shugaba Macron Jean-Yves Le Drian, ya ce lokaci ya yi da za a samu hadin kai da fahimtar juna tsakanin Faransa da Jamus, wadanda a baya ra'ayoyinsu kan Ukraine ke cin karo da juna.
Karin bayani:Scholz ya bukaci Turai ta kera makamai masu yawa
Wannan sabani na zama wata hanyar farantawa shugaba Vladimir Putin na Rasha, kuma na haddasa babban gibi ga Ukraine wajen kare kanta, in ji mashawarcin shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy na musamman Mykhailo Podolyak, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.