SiyasaTurai
Zelensky zai halarci taron tsaro na Jamus
February 16, 2024Talla
Shugaba Volodymyr Zelensky zai kawo wannan ziyara ne a Jamus da Faransa da nufin saka hannu kan wata yarjejeniyar tsaro da kasashen biyu sannan kuma da neman karin tallafin makamai da suka yi wa sojojin kasarsa karanci.
A yayin wannan garejen rangadi shugaba Zelensky zai halarci taron tsaro na shekara-shekara karo na 60 da za a fara a ranar Asabar a birnin Minich da ke Kudancin Jamus inda ake sa ran zai yi jawabi, kafin daga bisani ya je birnin Paris na kasar Faransa.
Wannan ziyara na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki kadan a cika shekaru biyu da Rasha ta kaddamar da mamayar Ukraine, kuma a daidai lokacin da dakarun Kiev ke fama da matsaloli a fagen daga, baya ga rudani a game da tallafin makamai da Amurka ke bai wa kasar.