Farfagandar kasar Rasha a Afirka
November 30, 2022Duk da cewar farfagandar Kremlin har yanzu takaitacciya ce, yunkurin na samun karbuwa cikin sauri. Wannan dai tamkar somin tabi ne kawai, kafin a fara yada karin farfagandar Rasha daga babban birnin tattalin arzikin Afirka ta Kudun Johannesburg. Tashar RT, wacce a da aka fi sani da kafar yada labaran kasar mai suna "Russia Today" kuma aka dakatar da ita a Turai da Birtaniya da Kanada tun bayan yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine, na son kafa shalkwatarta ta harshen Turanci ta farko a Afirka ta Kudu.
An kawar da shirin kafa cibiyar yada labaran Rasha daga birnin Nairobi zuwa kudanci kuma ana jin ra'ayin shugaba Vladmir Putin game da al'amuran kasa da kasa a Afirka, musamman ganin yadda kasashen nahiyar da dama suka yi shiru game da yakin da ya ke yi. Katafaren kamfanin nishadantarwa na Afirka ta Kudu MultiChoice wanda ke alfahari da wani babban gidan talabijin na tauraron dan Adam a yankin Kudu da Saharar Afirka, ya nesanta kansa da kafar yada labaran kasar Rashan mako guda bayan fara yakin sakamakon takunkumin da kasashen yamma suka kakabawa Rasha.
Karin Bayani: Amincewa da kudiri kan yankunan Ukraine
Sai dai har yanzu Putin na fadada tasirinsa ta hanyar yada labarai, a wasu kasashen Afirka da ke da alaka da Rasha tun zamanin tsohuwar Tarayyar Soviet ciki har da Afirka ta Kudu. Yaya tasirin wannan farfagandar ta Kremlin ke gudana a nahiyar, kuma ta yaya kafofin yada labarai ke mayar da martani? Christoph Plate shi ne shugaban sashin yada labarai na gidauniyar Konrad Adenauer mai kula da yankin Kudu da Saharar Afirka a Johannesburg ya ce, wasu na nuna halin ko-in-kula wasu kuma sun fito fili sosai wajen sukar yakin da Rasha ke yi a Ukraine.
Amma Guido Lanfranchi mai nazari kan irin tasirin da Rasha ke yi a nahiyar Afirka na da ra'ayin cewa: "A lokaci guda yana da kyau a lura cewa kasancewar Rasha a nahiyar Afirka, na kara samun bunkasa cikin sauri a dukkan fannoni. Yanke huldar da kasashen yammaci suka yi da Moscow na iya kara assasa wannan yanayin, yayin da kasar Rasha ke neman sababbin abokan kawance a matakin kasa da kasa. A dangane da haka ya kamata a lura da cewa, Rasha tana kara samun bunkasa sosai a nahiyar Afirka."
Karin Bayani: Kawayen Rasha a Afirka
Ta fuskar diflomasiyya, Rasha na yawan gayyatar shugabannin kasashen Afirka a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan. Ta wannan hanyar Rasha ta kulla hulda tare da kwararrun Afirka wadanda suka yi karatu a Moscow a zamanin yakin cacar baka, godiya ga tallafin karatu na tsohuwar Tarayyar Soviet. Da yawa daga cikinsu sun kasance cikin masu mukaman shugabancin Afirka kamar a Afirka ta Kudu da Angola da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kuma sun ci gaba da hadin gwiwa musamman tun lokacin da tsohuwar Tarayyar Soviet din ta tallafawa kungiyoyin da ke fafutukar neman 'yanci a Afirka.