1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Putin ya gargadi kasashen Yamma kan yakin Ukraine

February 29, 2024

Shugaban Putin na Rasha ya yi kwakkwaran kashedi ga kasashen Yammacin duniya tare da yin barazanarar yin amfani da makamin nukiliya muddin suka yi kuskuren shiga gadan-gadan cikin yakin da yake a Ukraine.

https://p.dw.com/p/4d1dW
Poutine ya gargadi kasashen Yamma kan yakin Ukraine
Poutine ya gargadi kasashen Yamma kan yakin UkraineHoto: Evgenia Novozhenina/REUTERS

A yayin jawabinsa na shekara-shekara, Shugaba Vladimir Putin ya yi martani da kakkausan lafazi ga kalamen shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron na yiwuwar aike wa da sojojin kasashe kawayen Ukraine domin dafawa dakarun kasar. 

Karin bayani: Zelensky ya sha alwashin galaba kan Rasha

Shugaba Putin ya kuma zayyana manufofin da Rasha ta saka a gaba yayin da ya rage makonni biyu a gudanar da zaben shugaban kasar da aka riga aka san zai lashe bayan ya kawar da duk wadanda za su iya kawo masa cikas.

Bayan ya yaba da nasarorin da dakarunsa ke samu a kan takwarorinsu na Ukraine, shugaba Putin ya kuma ce a shiye Rasha take domin tattaunawa da Amurka kan batutuwan da suka shafi maradun kasashen biyu.