1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Najeriya: Raguwar jiragen sama da ke jigila

Muhammad Bello L
October 25, 2024

Hukumar Gudanarwar Harkokin Jiragen Sama ta Najeriya, ta ce ana samun raguwar jiragen sama da ke zirga-zirga a cikin kasar da kusan kaso 50 a yanzu.

https://p.dw.com/p/4mFPr
Najeriya | Jiragen Sama | Kalubale
Fasinjoji na fuskantar tarin kalubale a filayen jiragen saman NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Hukumar Gudanarwar Harkokin Jiragen Sama ta kasa a Najeriyar ta NCAA, ta ce kamfanonin jiragen sama da dama a kasar sun yi rauni sosai kuma hakan shi ne ainihin abin da ke janyo matsalolin da fasinjoji ke samu yayin duk wata tafiya da za su yi a kasar. Matsalolin kuma da suka hadar da na rashin martaba ka'idar lokacin shigar fasinjojin cikin jirgi da ma tashinsa da kamfanonin na jiragen sama kan sanar a rubuce, ta yadda za ka ga fasinjoji na ta jiran gawon shanu a filayen jiragen sama. A lokuta da dama ma, sai dai kawai fasinjoji su ji kamfanin jirgi na sanar da soke tafiya baki daya.

Najeriya | Jiragen Sama | Kalubale
Kamfanin jiragen sama na Chanchangi, na cikin wadanda aka daina jin duriyarsu a Hoto: George Osodi/AP Photo/picture alliance

NCAA din dai ta ce kamfanonin jiragen sama da dama a kasar sun zabge yawan jiragen da su ke da su, inda ma za ka ga wasu Kamfanonin jirage biyu kacal su ka rage musu. Hakan ta sanya ba sa iya yin sufuri fiye da sau biyu, abin da kwararru suka ce shi ne tabbacin an shiga rigima ke nan. Kamfanonin jirage dai yanzu a kasar na kukan yadda suke ta fama da kiki-kakar sauyin kudi a kasuwar canji ta FOREX da gazawar iya fitar da jiragen nasu zuwa kasashen da a kan yi musu gyare-gyare na lokaci zuwa lokaci, sannan wadanda suka iya fita wajen domin gyaran sun kasa dawo da su sakamakon tsada ta dalilin musayar kudi baya ga tsadar man jirgin da saura kalubale.