SiyasaTurai
Rasha ta sake kai hare-hare kan tashoshin makashi a Ukraine
March 30, 2024Talla
Wasu yankunan kasar Ukraine uku, sun fuskanci daukewar wutar lantarki bayan hare-hare da dakarun Rasha suka kai kan wasu tashoshin samar da wutar a jiya Juma'a.
Hukumomi a Ukraine sun ce akwai hari na makami mai linzami da kuma na wani da aka kai da jirage marasa matuka a kan tashohi da dama wadanda ke samar da makamashin na lantarki.
Daga ciki har da wasu tashoshi na dam-dam da wadanda ke amfani da tururi.
A baya dai Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine ya kwatanta hare-haren Rasha kan cibiyoyin samar da wutar lantarki a matsayin wani ''ta'addanci na makamashi.''
Jakadan Amurka a Ukraine din ma ya yi Allah wadai da hare-haren da Rasha ke kaiwa a kan cibiyoyin na lantarki da miliyoyin mutane suka dogara a kansu.