1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Barazanar korar ma'aikata

June 13, 2024

Sa'o'i kalilan da kalaman shugaban Tarayyar Najeriya na amincewa da sabon mafi karancin albashi a kasar, takaddama ta barke a tsakaninsu da 'yan kodago.

https://p.dw.com/p/4h0kO
Najeriya | NLC | Abuja
Rikicin kungiyar kodogon Najeriya da gwamnati, ya dauki sabon saloHoto: Uwais/DW

A cikin yanayi na ba-zata ne dai, shugaban Tarayyar Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya ayyana nasara, kan batun samar da mafi karancin albashi ga miliyoyin ma'aikatan kasar. To sai dai kuma tun ba a kai ko'ina ba dai kungiyoyin kodagon suke fadin ko dai tsufa ko kuma rashin sani, ya sanya Tinubu yin kalaman da babu gaskiya a cikinsu. 'Yan kodagon dai sun ce, ba su kai ga cimma matsaya da masu mulkin Najeriyar kan sabon albashin da ke zaman gada tsakanin ma'aikata da talaucin da ke barazana ga rayuwa da makoma ba. Matsayin kuma da ga dukkan alamu ya harzuka masu mulkin da ke barazanar korar ma'aikata, kafin iya kai wa ga biyan naira dubu 250 a matsayin mafi karancin albashin. Abujar dai ta ce tilasta biyan bukatar 'yan kodogon, na iya kai wa ga gurgunta tattalin arzikin kasar da ya dauki lokaci cikin halin rudu. Dakta Muttaka Yusha'u dai na zaman jami'i na gangami da wayar da kai na kungiyar kodagon kasar NLC, kuma ya ce batun na sallamar ma'aikatan na zaman kokari na zare ido ga masu aikin kasar a cikin takkadamar mai zafi.Sabuwar takkadamar dai na kara fitowa fili da irin girman rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu a Tarayyar Najeriyar, inda zare tallafin man fetur da sakin darajar Naira ke neman gaza kai wa ya zuwa samar da kudin da masu mulkin ke fatan su gani. Duk da cewar dai 'yan kasar sun kalli karin kisan kudin da ya kai kusan kaso 300 a cikin 100 na tsadar rayuwa sakamakon matakai na Abujar, mahukuntan Najeriyar na kallon karin kudin shigar da ba su kai kaso 50 cikin 100 a lalitarsu ba. Abdul Aziz Abdul Aziz dai na zaman mataimakin kakakin gwamnatin tarayyar, kuma ya ce gwamnatin ba ta da niyyar ta kwashe dukiyar kasar cikin sunan aiki. Abujar dai na korafin biyan kaso mafi karancin albashin na iya lashe abun da ya kai kusan kaso 30 cikin 100 na daukacin kasafin Najeriyar, kasar da ke da jerin bukatu walau na lafiya ko Ilimi da ma batun tsaron da ke zaman barazana mai girma.

Najeriya | Naira | Tattalin Arziki | Gwamnati | 'Yan Kodogo
Darajar Naira na hawa da sauka a NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW