1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An shiga rudani a Maiduguri da ke Najeriya bayan rufe hanya

October 13, 2020

A Najeriya an shiga rudani da damuwa bayan da sojoji sun rufe hanyar daya tilo da ta saura wacce ake shiga Maiduguri daga wasu wurare saboda kaddamar da wasu hare-hare kan mayakan Boko Haram da ke yankunan.

https://p.dw.com/p/3jsVU
Nigeria Soldaten in Damboa
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis


Ba zato ba tsammanin ne dai al’ummar su ka wayi gari da rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu da wasu hanyoyi a jihohin  Borno da Yobe abin ya haifar da damuwa saboda muhimmancin hanyar wacce ita ce daya tilo da ta saura da ke hada Maiduguiri da sauran sassan arewacin Najeriya. Daruruwan Motoci ciki har da wadan su ka dauko kayayyakin masarufi da kuma masu jigilar fasijnja sun makale a hanya inda tuni wasu danyun kayayyaki suka fara baci dabbobi kuma da ake shirin fita da su suka fara galabaita.

Karin Bayani:  Borno: Martani dangane da hari kan gwamna
Harkokin  sufuri da na yau da kullum sun tsaya cik a Maiduguri tun lokacin da aka rufe annan hanyar duk da dai Sojojin sun dan bude hanya matafiya da ba su san da rufewar ba suka fito daga wasu garuruwa su samu shiga ko fita birnin. Kungiyoyin fararen hula sun bayyana damuwa kan wannna mataki wanda suka ce zai kara jefa al’umma da yaki Boko Haram ya daidai cikin mawuyacin hali. Ambasada Ahmed Shehu shi ne shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula na jihar Borno wanda ya nuna damuwa.


Kungiyoyin ‘yan kasuwa sun ce matakin zai cutar da su musamman masu danyen kaya wadan da tuni su ka fara lissafin abin da su ka fara yin hasara. Wannan yanayi ya haifar da karancin kayayyakin masarufi a kasuwanni wanda kuma zai iya kara jefa al’umma cikin mawuaycin halin bayan wanda suke ciki. Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa da sojojin suka fitar da ke nuna tsawon lokaci na rufe wannan hanyar inda masu fashin baki na ganin ya kamata a gaggauata bube wannan hanya saboda muhimmancin ta domin gujewa jefa al’umma cikin hadari.

Nigeria Autobombe Polizeistation
Hoto: Reuters