Tunkarar rashin tsaro gadan gadan a Najeriya
May 11, 2021Akalla 'yan sanda 12 ne aka hallaka a karshen makon da ya shige a jihohin Abia da Akwa Ibom kadai, a wani abun da ke nuna ta'azarar rashin tsaro a sassan Kudu maso Gabashin kasar da dan uwansa da ke Kudu maso Kudu.
Ana dai kone caji ofisoshin 'yan sandan sannan kuma ana binsu ana kisa kamar 'ya'yan bera, abun kuma da ya tada hankalin majalisar tsaron kasar da ke gudanar da taro na uku cikin tsawon kasa da makonni biyu.
Karin bayani: Najeriya: Zargin yankurin juyin mulki
Majalisar manyan hafsoshin soja da jami'an tsaro dai ta kare zamanta a nan a Abuja tare da shugaban kasar amincewa da wani shiri na tunkarar kisan 'yan sandan.
Duk da cewar dai basu fito fili domin ayyana irin sabbin matakan da suke shirin dauka ba, babban sufeton 'yan sanda na kasar Usman Baba ya ce, ana shirin tura jami'an 'yan sanda na musamman da kara yawan 'yan sanda a yankunan guda biyu da nufin tunkarar ayyukan tsagerun awaren da ke dada cin karensu har gashinsa.
To sai dai in har Abujar tana da lafiya a idanu na jami'an tsaron, fadar gwamnatin kasar ta ce an nemi kai hari a gidajen wasu manyan jami'an gwamnatin kasar guda biyu.
Batun na tsaro dai na zaman batu mafi girma da ya mamaye bakunan 'yan kasar da ke masa kallon gazawa a bangare na gwamnatin kasar.
Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe mutum 17 a Najeriya
Su kansu gwamnoni na kudancin kasar 17 dai sun gana a garin Asaba ta jihar Delta da nufin kallon matsalar da sannu a hankali ta watsu zuwa sashen na kudu.
To sai dai kuma a fadar mashawarcin tsaron kasar janar Babagana Monguno gwamnatin Najeriyar na sauya dabara da nufin shawo kan rikicin da ke ta kara karuwa cikin kasar a halin yanzu.
"Mun yanke hukuncin kaucewa daga al'adar mu ta baya da a cikinta mukan bayyana wasu daga cikin dabarunmu na wannan yaki. Tabbas muna cikin yanayin da muke yakar makiyan da bamu sansu ba. Umarnin shugaban kasa shi ne tunkarar matsalar, kuma yana kallon cewar babban aikinsa shi ne tabbatar da rayuwar kasa, a cikin yanayin yakin. A saboda haka ya baiwa manyan hafsoshin tsaro karkashin shugabancin babban hafsan tsaron kasa umarni kan abun da ya kamata su yi. Haka su ma jami'an tsaron farin kaya na amfani da matakai na dakile wannan matsala".
To sai dai kuma ko ya zuwa ina sabuwar dabarar wasan buyan ke iya kaiwa ga tabbatar da kai karshen matsalar dai, a tunani na manyan hafsoshi na tsaron akwai alamun haske a kokari na sake kwantar da hankula cikin kasar.
Karin bayani: Najeriya: Barazarar tsaro ga zabukan 2023
Janar Lucky Irabor dai na zaman babban hafsan tsaron kasar da kuma ya ce abubuwa da dama sun faru a cikin 'yan watannin da suka wuce.
"Ga wadanda suke bin diddigin abun da ke faruwa a Arewa maso yamma alal ga misali, sun san cewar an hallaka shugabannin 'yan ina da kisan da daman gaske a cikin matakan da muke dauka da kuma kokarin ceto mutanen da aka sace, matakan kuma da bamu son mu daga murya kansu, amma kuma su na da babban burin cika umarnin shugaban kasa, shi yasa zaku ga an samu sararawa a cikin wannan yanki. A yankin Arewa ta Tsakiya ma an yi da dama, haka ma a Kudu maso Gabas, a gaba daya ina da imanin cewa muna samun nasara".