Sabon firaminista ya yi alkawarin sake gina kasar
July 5, 2024Sarki Charles na III ya bukaci Starmer da ya kafa gwamnati yayin wani taro a fadar Buckingham, bayan ya nada tsohon lauyan mai kare hakkin dan Adam dan shekaru 61 da haihuwa a hukumance a matsayin Firaministan Birtaniya. Daruruwan masu fafutuka na jam'iyyar Labour ne suka yi jerin gwano a Downing Street yayin da Starmer ya isa a matsayin firaminista na farko tun bayan Gordon Brown a shekarar 2010. Sabon Fraministan Birtaniyar ya ce wajibi ne a hada kai wajen samar da irin sauyin da al'umma ke muradi domin ciyar da kasar gaba.
Karin Bayani: Birtaniya: Sabon firaminista ya kama aiki
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya mika sakon taya murna ga sabon firaminista Keir Starmer yayin wani taron manema labarai a birnin Berlin. Ya ce a matsayin gwamnati, Berlin za ta yi aiki da gwamnatin Birtaniya da kyau, haka lamarin yake a cikin shekarar da ta gabata kuma yana da kyau a san cewa, hakan zai dore zuwa nan gaba.
A daya bangare ministan Scotland John Swinney ya ce sakamakon babban zaben Birtaniya yana da matukar tsauri ga jam'iyyarsa mai mulki ta (SNP) yayin da ta rasa kujeru da dama. Ya zuwa karfe uku agogon GMT dai kusan dukkan mazabu a Scotland sun sanar da sakamakon da ya nuna cewa jam'iyyar SNP ta rike kujeru tara ne kacal daga cikin 57, kasa da 43 kafin a gudanar da zaben.
Sakamakon dai shi ne mafi muni ga jam'iyyar SNP a zaben 'yan majalisar dokokin Birtaniya da aka gudanar tun shekara ta 2010, kuma babban koma baya ne ga yunkurin da ta ke yi na sake gudanar da zaben raba gardama na 'yancin kai, yayin da jam'iyyar Labour da ta sake farfadowa ta samu nasarori a tsoffin yankunan kasar.
A yanzu haka dai Birtaniyar na cikin hali na matsin tattalin arziki kamar sauran kasashen duniya, sai dai sabuwar gwamnatin ta Labour ta yi alkawarin daukar matakin bunkasa tattalin arzikin kasar bayan da jam'iyyar ta masu ra'ayin rikau ta yi nasara a babban zaben kasar. Sai dai ana ganin cewar wannan yunkuri na iya samun cikas saboda karancin kudi, biyo bayan kashe makudan kudade da gwamnatin Conservative da ta gabata ta yi don kare miliyoyin ayyuka yayin barkewar cutar ta Covid.