1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sama da mutum biliyan daya na cikin mummunan talauci - MDD

October 17, 2024

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matalautan sunfi yawa ne a kasashen Afirka da kudancin Asiya.

https://p.dw.com/p/4ltRt
Hoto: Florian Gaertner/IMAGO

Hukumar kula da harkokin ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ta bayyana cewa mutum sama da biliyan daya na fama da matsanancin fatara a duniya.

Rahoton da hukumar ta fitar ya kara da cewa yara ne suka fi fadawa cikin talaucin da aka gano na addabar mutane a sassa daban-daban na duniya musamman a shekarun baya-bayan nan.

Karin bayani: Wa ke morar agajin gwamnati a Najeriya?

Rahoton ya yi amfani da ma'aunai da suka hada da rashin isassun gidaje da muhalli mai tsafta da lantarki da man girki da abinci mai gina jiki da kuma zuwa makaranta.

Har ila yau, rahoton wanda aka wallafa a cibiyar kula da yaduwar talauci da kuma ci gaban al'umma ta Oxford Poverty and Human Development Initiative dake Burtaniya, ya nuna talaucin ya rubanya har sau uku a kasashen da ke fama da yaki.

Karin bayani: Kasashe 26 na fama da bashi mafi muni

A cewar rahoton, duniya bata taba ganin rikice-rikice da ta gani a shekarar 2023 ba tun bayan yakin duniya na biyu.

Babban jami'in kula da alkaluma na hukumar ta UNDP Yanchun Zhang, ya ce  kashi 83.2% na mutanen da suke fama da talaucin a duniya 'yan nahiyar Afirka ne da kuma kudancin Asiya.