Najeriya: Wa ke morar agajin gwamnati?
September 10, 2024To sai dai kuma daga duk alamu, zahirin da ke cikin kasar ya bambanta a tsakanin miliyoyin al'ummar da ke zaman jiran tasirin gwamnati. Ko a cikin wannan mako dai, gwamnatin jihar Kano ta yi korafin karkatar da tallafin zuwa batu na siyasa bayan da Abuja ta mika daukacin abincin jihar zuwa ga jiga-jigan jam'iyyar APC ta adawa. Kuma ko bayan masu takama da adawar su kansu jihohin APC sun ikirarin batan dabo na abincin da kila ma kudin tallafin da ke da babban burin tasiri ga rayuwa da makoma, amma kuma ke neman komawa siyasa a cikinTarayyar Najeriya a halin yanzu.
Karin Bayani: Najeriya: Haraji kan zambar kudi ta Internet
Inuwa Yahaya dai na zaman gwamnan jihar Gombe kuma shugaban kungiyar gwamnonin arewacin kasar, daya kuma a cikin jihohin da ke fadin da sauran sake cikin batun na tallafi mai tasiri. Kama daga shinkafa 'yar kyauta ya zuwa mai saukin da ta kai kusan kaso 50 cikin 100, ko bayan kudi da za a bai wa talakawa, gwamnatin kasar ta raba agaji da daman gaske tun bayan zare tallafin man fetur. Wani bashin Bankin Duniya na dalar Amurka miliyan 700 ne dai, Najeriya ta ce tana fata zai kwantar da zuciya.
To sai dai kuma daga duk alamu mahukuntan Najeriya na da sauran tafiya, bisa hanyar cika burin sanyi a rayuwa ta da dama. Miftahu Yahaya dai na zaman wani mai zaman jira na tallafin, kuma ya ce ko a makwabta babu duriyar shinkafar. Ya zuwa yanzun dai Najeriya tana kallon karuwar kudin shiga sakamakon matakan zare tallafin da ma ragowar jari hujja da ke dada kwashe kudi daga aljihun tallaka, tare da mai da su zuwa wurin 'yan mulki na kasar. Sama da Naira Triliyan biyar ne dai, kwararru suke fadin sun fito a hannu 'yan kasar kuma sun koma ga gwamnatin bayan zare tallafin man fetur.
Karin Bayani: Saukar farashin kayan abinci a Najeriya
A wannan mako Abuja ta yi bikin tara Naira Tiriliyan daya da rabi, daga haraji na mai saye cikin tsawon watanni uku na zango na biyu na shekarar bana. Farfesa Kamilu Sani Fagge dai kwarrare ne bisa batun mulki a kasar, kuma ya ce yawan kudin ba shi da tasiri ga rayuwa da makoma cikin kasar. Wata kiddidiga ta Bankin Duniya dai ta ce a yayin da kasar ke dada samun kudin shiga, shi kansa talaucin na ta karuwa. Kuma talakawa cikin kasar sun haura miliyan 100, bayan zare tallafin da kyale Naira ta kasar goga kafada da kudin kasashen ketare a cikin neman daraja.