Sarki Charles na Ingila na ziyara a Faransa
September 20, 2023Sarki Charles na Burtaniya ya sauka a birnin Paris a yau don fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku, inda zai gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron don sake farfado da alakar da ke tsakanin kasashensu biyu da ta jima cikin halin zaman doya da man ja, musamman ma tun bayan ficewar Burtaniyar daga kungiyar Tarayyar Turai.
An dai shirya liyafar ban girma ga a yayin ganawar jagororin biyu, inda aka gayyato fitattun jarumai da 'yan wasa daban-daban 'yan asalin Burtaniya da Faransa, ciki har da tsohon mai horas da 'yan wasan Arsenal, Arsene Wenger da Didier Drogba na Cote'dIvore.
A baya dai Sarki Charles ya so yin bulaguronsa na farko tun bayan darewa kan gadon sarauta zuwa Faransa a cikin watan Maris din da ya gabata, to amma ya soke ziyarar sakamakon zanga-zangar kin jinin sauya tsarin Fansho da aka gudanar a Faransa a lokacin.