Satar mutane na kara samun gindin zama a Najeriya
March 18, 2024Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan dauke da muggan makamai sun yi wa yankin na Kajuru kawanya tare da sace mutane da dama, lamarin dai na zuwa a daidai lokacin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke fuskantar matsin lamba daga ciki da wajen kasar kan yadda ake garkuwa da mutane ba kakkautawa a lokacin gwamnatinsa.
Karin bayani: Sojin Najeriya sun lashi takobin kubutar da daliban Kuriga
Shugaban karamar hukumar Kajuru a jihar ta kaduna Ibrahim Gajere, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa 'yan bindigar sun yi awon gaba da mutane kimanin 87.
Karin bayani: Tinubu ya yi watsi da biyan kudin fansa ga 'yan fashi
Yankin na Kajuru na da nisan kilomita 150 wato mile 93 kenan daga garin Kuriga da aka sace dalibai kimanin 250 a farkon wannan watan na Maris.