1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Najeriya sun lashi takobin kubutar da daliban Kuriga

March 11, 2024

Dakarun sojin Najeriya sun shiga dazuka domin kubutar da daliban makarantar Kuriga sama da 300 da 'yan bindiga masu dauke da makamai suka sace su a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4dPFH
Sojojin Najeriya
Sojojin NajeriyaHoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaye sunanta, ita ce ta ce tuni dakarun sojin Najeriya suka bazama cikin dazukan da ke yankin domin kubutar da daliban na Kuriga, tare da bayar da tabbacin ceto su nan ba da dadewa ba.

Karin bayani: Tinibu ya yi Allah wadai da sace dalibai

Majiyar ta kuma ce kawancen dakarun sojin kasa da na sama da jami'an tsaron farin kaya har ma da jami'an sa-kai na bijilante ne ke cikin wannan fadi tashin domin kubutar da daliban na Kuriga.

Karin bayani: Kaduna: Neman mafita ga matsalolin Najeriya

Wani kamfani mai suna SBM da ke aikin tattara bayanan tsaro a jihar Legas, ya ce sama da mutane 4,500 ne aka yi garkuwa tun bayan hawan shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu kan kargar mulkin kasar.