1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamanceceniyar Moscow da Tehran

July 19, 2022

A yayin ziyararsa a Iran, Shugaba Vladmir Putin na Rasha zai tattauna batun makamai da jirage marasa matuka da Iran za ta aikewa kasar, amma a cikin sharhin da ya rubuta Kersten Knipp DW ya nuna tababar haka.

https://p.dw.com/p/4EMC0
Ganawa | Vladimir Putin da Ibrahim Raisi
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Iran Ibrahim RaisiHoto: Iranian Presidency/Zuma/picture alliance

Kersten Knipp ya fara sharhin nasa ne yana mai cewa. Me za a tattauna yayin ziyarar shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a Tehran? In har za a yarda da bayanai a hukumance daga kasashen biyu, tabbas babu wani abu mai kama da mika jiragen yaki marasa matuka da Iran ta kera ga Rasha. A makon da ya gabata, Amirka ta sanar da cewa an shirya tataunawa kan batun.

Mai bai wa shugaban AmirkaJoe Biden shawara kan al'amuran tsaro Jake Sullivan ya nunar da cewa, sun samu rahoton Iran na gaggawar kera daruruwan jiragen marasa matuka ciki har da wadanda za su iya safarar makamai.

Duk kasashen biyu sun musanta wannan batu, inda yayin da yake amsa tambayar 'yan jarida kakakin fadar mulki ta Kremlin Dmitri Peskov ya nunar da cewa babu batun tattauna abin da ya shafi jirage marasa  matuka yayin ziyarar. Shi ma ministan harkokin kasashen ketare na Iran Hussein Amirabdollahian wanda ya tabbatarwa da Ukraine cewa Tehran ba za ta aike da jirage marasa matuka zuwa Rasha ba, ya bayyana batun da wata farfaganda ta Amirka.

Kersten Knipp
Kersten Knipp na tashar DW

Sai dai Amirka na kan bakanta, inda Sullivan ya tabbatar da cewa akwai shaidu da ke nuna sau biyu wakilan kasar Rasha na ziyartar karamin filin jirgin sama a Iran tare da yin nazari kan ci-gaban da aka samu a shirin kera jirage marasa matuka na Iran da ma duba wasu makamai na zamani da Iran din ta kera.

Sai dai kuma abu ne mai matukar wahala a amince da bayanai a hukumance daga kasashen biyu. Ga misali, gabanin kaddamar da yaki a Ukraine wani babban jami'in gwamnatin rasha ya musanta hakan, kuma Rasha ta kai harin. Idan muka koma kan Iran, a 'yan kwanakin nan ta cire wasu kyamarori biyu a cibiyarta ta sarrafa makamashin nukiliya, abin da ke nuni da cewa Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya IAEA ba za ta samu bayanan abin da Iran ta aikata a wannan cibiyar a shekara ta 2021 da ta gabata ba. Idan aka hada wadannan batutuwa biyu, za aga da wahala a amince da bayanansu kan batutuwan da za su tattauna ya yin ziyarar.

A zahiri, maganar Iran ka iya bai wa Rasha  jirage marasa matuka abu ne mai yiwuwa. Mahukuntan Moscow da na Tehran, na matukar adawa da duk wani 'yanci na siyasa da kuma bin doka da oda. Batun 'yan kasa ka iya samun bayanai ta hanyoyin da suka amince da su ko kuma fadar ra'ayinsu a bainar jama'a, ba abu ne mai yiwuwa ba.

Iran | Jirage Marasa Matuka | Kerawa
Iran ta shahara wajen kera jirage maraasa matuka da makamai masu linzamiHoto: Iranian Army Office/ZUMA/IMAGO

Yadda kasashen ke mayar da martani ga masu adawa ko suka gare su, ya bayyana a jadawalin kasashen duniya da ke bin tafarkin doka na 2021, inda Rasha ta kasance ta 101 cikin 139 yayin da Iran ta kasance ta 119. Haka ma batun yake a jadawalin kasashen duniya kan cin-hanci da karbar rashawa na 2021 da Transparency International ta fitar, inda Rasha ta kasance ta 136 cikin kasashe 180 yayin da Iran ke a matsayi na 150.

Haka kasashen biyu ke bayyana kansu a matsayin makiya dimukuradiyya da bin doka da oda a duniya, kuma kusan a shirye suke su yi duk mai yiwuwa. A  Siriya, kasashen biyu sun marawa gwamnatin mulkin kama-karya ta Bashar al-Assad. Tun lokacin juyin-juya halin kasashen Larabawa na shekara ta 2011, gwamantin Assad ke da alhakin kisan daruruwan mutane a sansanin gwale-gwale na kasar.

Rasha da Iran ba su yi kasa a gwiwa ba wajen marawa wannan gwamnati baya da dukkan karfinsu, domin murkushe 'yan adawa. Abu ne mai yiwuwa a tattauna batun jirage marasa matuka da suka hadar da na yaki a Tehran, kasashen biyu na da manufofi guda musamman wajen kin bin tafarkin dimukuradiyya da kuma bin dokokin kasa da kasa.