Sayar da kadarorin gwamnatin Najeriya na cikin rudani
September 27, 2016Yanayi na koma baya da ke fuskantar tattalin arzikin Najeriya ya sanya tado da batun sayar da kadarorin gwamnati domin samun kudadden gudanarwa musamman na aiwatar da kasafin kudin kasar abin da kungiyar kwadago ta ce ba ta hango mafita daga abin da ta kira rashin dabara. Comrade Nuhu Abbayo Toro jigo a kungiyar kwadago kana mataimaki na musamman ga shugaban kungiyar, wanda ba za su goyo bayan shirin gwamnatin ba.
Tuni dama wannan lamari na ci gaba da haifar da cece-kuce a kasar musamman ganin kara shiga yanayi na halin wahalar tattalin arziki. Alhaji Shattima Umar Abba Gana shi ne shugaban hukumar kula da tattara kudadden shiga da rarrabasu ta Najeriya ya ce a yi taka tsantsan.
To sai dai a yayain da wasu masana tattalin arziki ke kashedi ga gwamnatin da ta guji tunanen daukan wannan mataki, ga Mallam Abubakar Ali masani a kan tattalin arzikin Najeriya na mai bayyana cewa ba a nan ma matsalar take ba.
Tuni dai kwarrau a fanin tattalin arzikin irin su Farfaesa Charles Sulodo ke bayyana tunanen sayar da kadarorin gwamnatin a matsayin babban kuskure, har zuwa wannan lokacin shugaban Najeriya bai ce komai ba kan wannan batu.