Shugaba al-Sisi na Masar na son a tsagaita wuta a Gaza
October 27, 2024Shugaban na Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya ce, a cikin kudurin yarjejeniyar za a sako wasu daga cikin fursononin Falasdinu da kuma wasu mutum hudu daga cikin wadanda Hamas ke tsare da su, tare da shigar da kayan agaji cikin Zirin Gaza da Isra'ila ta yiwa kawanya.
Karin bayani: Kasashen duniya na kira da a kawo karshen yakin Gaza
Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban Masar ya mika wannan bukata a bainar jama'a. Shugaba al-Sisin ya ce wannan matakin zai samar da ci gaba, kana idan yarjejeniyar ta kwanaki biyu ta fara aiki, za a cigaba da tattaunawa domin tabbatar da ita na din-din-din.
Sai dai kuma babu martani daga hukumomin Isra'ila ko kuma kungiyar Hamas wadanda ke gwabza yaki yau sama da shekara guda. Kasar Masar dai na zama babbar mai shiga tsakani a rikicin Gaza tare da kasashen Katar da kuma Amirka.