Shugaba Putin na ziyarar karfafa danganta a China
May 16, 2024Ziyarar Shugaba Vladmir Putin ta kwanaki biyu a China za ta mayar da hankali a kan wasu batutuwa da suka hada da batun rikicin kasarsa da Ukraine da ma wadanda suka shafi kasashen Asia da kuma ta batun kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Xi Jinping na kasar China ya sha alwashin farfado da dangantakar aiki kafada-da-kafada da kasar Rasha.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da Shugaba Vladmir Putin na Rasha ke yi a kasar.
A yayin ganawar farko da suka yi a babban zauren taro na Great Hall a Beijing, China ta sake jaddada cewar za ta ci gaba da zama kawa ta amana ga Rasha.
Wannan ziyara ta Putin a China da ke zuwa bayan ya sake darewa madafun iko a karo na biyar na aikewa da sako ga kasashen duniya kan irin shakuwar da ke tsakanin shugabannin biyu, da kasashen yamma ke nuna damuwa a kai.