Siyasar Jamus: Manhajar Tiktok na taka rawar gani ga matasa
May 6, 2024Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da ke yawan fuskantar barazana wajen amfani da shafukan sada zumunta ya dawo amfani da Tiktok gadan-gadan a watan Afrilun 2024, yayinda mataimakin shugaban gwamnatin Robert Habeck, ya rufa masa baya wajen amfani da manhajar duk da cewa a baya ya rufe shafukansa na facebook da Twitter domin dakile fuskantar fushin matasan zamani.
Karin bayani: Ranar Mata: 'Yancin zabe ga matan Jamus
Jam'iyyar AfD ce ke kan gaba wajen amfani da Tiktok da galibin matasa daga shekara 14 zuwa 29, da kuma kaso 22% na wadanda suka isa kada kuri'a ke rububin shiga jam'iyyar Alternative for Germany AfD.
Karin bayani: Jam'iyyun hadaka a Jamus sun gaza a zaben jihohin Bavaria da Hesse
Jamus na da kimanin mutune milyan 20 da ke amfani da Tiktok, a wani rahoton kididdiga da hukumomin kasar suka fitar, inda shekarun kaso 60% bisa 100 na masu amfani da manhajar, ya kama daga shekara 12 har zuwa 16 da kullum suke kan manhajar.