Siyasar sauya sheka a Tarayyar Najeriya
January 11, 2024A cikin tarihi na siyasar Najeriya dai, lokaci na kammala shari'un zabe na zaman mafi wahala ga masu adawa ta kasar.
An dai sha kallon kokari na sauyin sheka a bangare na masu adawar, ko dai a kokari na kauce wa ‘yunwa ko kuma rikicin cikin gida mai zafi. To sai dai kuma wata ziyarar kakaki ga dantakara na jam'iyyar PDP ta adawa a zaben shugaban kasar da ya gabata dai, na jawo dagun hakarkari a fagen siyasar Najeriyar a halin yanzu.
Bayan ziyarar da ya kai fadar gwamnatin kasar a Abuja, Daniel Bwala da ya jagoranci fada a kokari na dora Atiku bisa mulki, ya ce kasar ta dade ba ta ga shugaban da ke ta kokarin ceton lamura ba kamar Bola Tinubu. Daniel Bwalan da a baya ya kira shugaban da kalamai da ke da kamar wuya a maimaita su dai ya yi tsallen badake tare da nesanta kansa cikin rawar da ya taka a lokacin yakin neman zabe.
Kokarin warware matsalar cikin kasa ko kuma neman kare matsalar aljihu dai, Bwalan na zaman na baya-baya cikin jerin masu adawar da yanzu haka APC mai mulkin kasar ke yi wa karatun mesa. Ana dai kallon maimata salo irin na jam'iyyar PDP da a baya ta hadiye duk wani mai takama da adawa cikin kasar amma kuma ta kare a cikin mummunan rikicin cikin gidan da ya kare burinta na kaiwa 60 bisa mulki.
Ibrahim Abdullahi dai na zaman mataimaki na kakakin PDP na kasa, kuma ya ce sun hango ‘yar gidan jiya a bangaren APC mai hadiya amma kuma ba ta da hanyar ta kasayar da rubabbun yaya.
Ko ma ya zuwa ina masu tsintsiyar ke shirin su kai a kokarin kara yawan magoya bayan dai, sabon matakin dai a tunanin Abdullahi Tanko, jigo a cikin jam'iyyar APC na kama da yabon gwanin da ya zama dole.
Abun jira a gani dai na zaman tasirin sauyin shekar cikin kasar da ke da bukata ga adawa a kokari na inganta lamura da kila ma kare zarmiya ta masu mulki a kasar.