Sojojin Mali sun haramta al'amuran siyasa a fadin kasar
April 11, 2024Gwamnatin sojin Mali ta sanar da dokar haramta duk wani gangamin siyasa a fadin kasar, acewar mai magana da yawun sojojin Malin Abdoulaye Maiga a wata sanarwa da ya karanta ta kafar talabijin, inda ya kafa hujja da kudirin dokar sojin kasar da shugaba Kanal Assimi Goita ya rattaba hannu.
Karin bayani: Nijar: Sojoji sun ki cewa komai kan dage takunkumin ECOWAS
Matakin na shugaban mulkin sojin kasar Kanal Goita na zuwa ne a daidai lokacin da gamayyar jam'iyyun adawar kasar kimanin 80 suka rattaba hannu na hadin gwiwa wajen kalubalantar manufofin sojin a wata sanarwa hadin gwiwa da suka fitar a ranar 1 ga watan nan na Afrilu da muke ciki tare da bukatar dawo da kasar kan turbar dimukradiyya ba tare da bata lokaci ba.
Karin bayani: 'Yan ta'adda sun kai hare-hare a wasu sansanonin sojan Mali