Najeriya: Ta'asar rashin tsaro
May 10, 2023Rashin rashin tsaron dai ya janyo lalata kadarorin hukuma kama daga na man fetur a yankin Niger Delta, kuma ba'a kyale makarantun sashen arewacin kasar ba. Ko bayan rusa cibiyoyin samar da hasken wutar lantarki da ma uwa uba layin dogo, duk a cikin sunan rashin tsaro a Najeiryar da ke bukatar girma amma kuma ke kallon lalata muhimman kadarorin girman. Kuma kama daga tsagerun yankin Niger Delta ya zuwa masu takama da Boko Haram bayan dillalan kisa da satar shanu dai, Najeriyar ta ga baki a hannun masu ja da ikon hukuma cikin kasar tsawon lokaci. Sama da dalar Amurka miliyan dubu 200 ne dai Hukumar Kare Kadarorin Fararen Hula ta kasar ta ce an lalata, tun bayan sake dora dimukuradiyya bisa saiti a shekaru 20 da doriya. Adadin da ke kara fitowa fili da irin girman asarar da kasar ta yi, cikin batun rashin tsaron da ya dauki lokaci yana ta tarnaki ga kokairnta na dorawa zuwa gaba.
Kabiru Adamu dai na zaman shugaban kamfanin Beacon Consult da ke bin diddigin batun rashin tsaro a Najeriyar, kuma a cewarsa girman rikicin rashin tsaron ya wuce da sanin 'yan mulki. Kokari na kare dukiya da rayukan al'umma ko kuma kara shiga halin rudani, ana dai ta'allaka tafiyar hawainiya ga kokarin Najeiryar na ci gaba da karuwar asarar da kasar ke dibgawa da ayyukan na masu zunguro sama da karan. Ko bayan jan aikin sake ginin kadarorin dai, hankalin Najeriyar na ta karkata ga batar da kudin makamai a cikin neman kai karshen annobar rashin tsaron zuwa tarihi. Abun kuma da a fadar Dakta Hamisu Ya'u masanin tatttalin arziki a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya sa da kamar wuya iya kai wa ya zuwa sauyin da 'yan kasar ke zaman jira tsawon lokaci. Najeriyar dai ta share shekaru 24 a cikin fatan dimukuradiyyar Yamman na iya sauya rayuwa da kila makomar miliyoyin 'yan kasar da ke takama da arziki a ko'ina, amma kuma ke kallon karuwa ta yunwa da talauci da kila ma dimbin bashin da ke ta karuwa cikin kasar a halin yanzu.