1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matsayin tallafin aikin Hajji a Najeriya

Uwais Abubakar Idris SB
July 29, 2024

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta bayyana dalilan da suka sanya duk da Naira bilyan 90 da gwamnati ta bayar a matsayin tallafi ga alhazan kasar, kudin aikin Hajji ya yi sama.

https://p.dw.com/p/4isYM
Najeriya
Shugaban Hukumar aikin Hajji ta Najeriya Malam Jalal Ahmad ArabiHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta bayyana dalilan suka sanya duk da tallafi na Naira bilyan 90 da gwamnatin Najeriya ta bayar a matsayin tallafi ga alhazan Najeriya a aikin hajjin wannan shekara, to sai dai duk da wannan kudin, aikin Hajjin ya kai fiye da Naira milyan takwas, abin da ya sanya ‘yan majalisar dokokin Najeriyar bayyana za su gudanar da bincike.

Karin Bayani: Najeriya: Majalisa ta bukaci a rage wa Maniyyata kudaden hajji

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya ta yi bayani na yadda ta kashe wadannan kudade sisi da kwabo da gwamnatin Najeriyar ta bata bayan da kudin aikin Hajji ya yi tsada sakamakon tashin takardar kudi ta dalla da a lokacin aikin Hajjin ta kai fiye da Naira 1474.

Shugaban hukumar alhazan ta Najeriya Malam Jala Ahmed Arabi ya bayyana yadda a bisa lissafi na Naira da kwabo yadda suka kashe Naira bilyan 90 din da ko dai su tallafawa alhazan su dubu 18 da ba za su cika ko kwabo ba daga kudin aikin Hajji na Najira milyan 4.9 inda bisa amincewa suka fadada shi zuwa alhazai dubu 50.

Saudiyya | Masu aikin hajji
Masu aikin HajjiHoto: FADEL SENNA/AFP/Getty Images

An dai wo cha a kan adadin kudin da gwamnatin ta bayar a matsayin tallafi ga mahajattan na Najeriya saboda tsadar da takardar kudi ta dala ta yi a lokacin aikin hajii. Wannan ya sanya majalisar dokokin Najeriya ta nada tawaga ta musamman don su bincika abin da ya faru da a yanzu ma suke yunkurin sake bin kadin lamari.

Batun abincin alhazai da kudin guzuri ne dai ya fi daukar hankali abin da Hukumar alhazan ta Najeriya ta bayyana da cewa duka batu ne na tsadar da dalar ta yi ya shafi, domin bayan alkawari da bankunan Najeriya sai lamarin ya canza.

Shugaban Hukumar alhazan ta Najeriya Malam Jalal Arabi ya bayyana matakai na gaba da suka tsara dauka don fadada lamarin. A yanzu dai Hukumar alhazan Najeriyar ta sanar da fara shiri na aikin Hajjin shekara mai zuwa ta 2025.