1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar dangantakar Afirka da Turai

Martina Schwikowski BAZ/LMJ
June 9, 2021

Masu ruwa da tsaki daga nahiyar Afirka, za su gana da takwarorinsu da ke kasashen Turai domin lalubo sabuwar hanyar karfafa dangantaka tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/3uf5y
The Africa Roundtable
Kasashen EU da na Afirka, na shirin samar da sabuwar dangantaka a tsakaninsuHoto: Danilo Höpfner/GPI

Taron dai na zaman irinsa na farko tun bayan annobar corona a duniya, annobar da ba tattalin arzikin nahiyar Afirka kawai ta yi wa illa ba har ma da na kasashen da ke da karfin tattalin arziki. Sai dai kuma a hannnun guda ana iya cewa ga alamu annobar ta bude wa duniya ido, lamarin da ya kai ga masu ruwa da tsaki a nahiyar Afirka da Turai ke fadi tashin ganin sun mayar da asarar ta zama riba a wanan yanayin Mo Ibrahim

Karin Bayani: Karfafa dangantakar Afirka da Turai

Yayin tattaunawar dai, bangarorin biyu za su dauki matakan farfado da nahiyoyin biyu. Guda daga cikin mahalarta wannan taron shi ne shahararen attajirin Afirkan nan na kasar Sudan Mo Ibrahim. Da yake jawabi gabbanin taron, ya bayyana bukatar samar da hanyoyin inganta fasahohin kimiya domin samar da ayyuka ga al'umma, wanda hakan zai taimaka wajen farfado da tattalin arziki. Sai dai ya koka a kan matsalolin tsaro da nahiyar ke fuskanta.

Mo Ibrahim | britisch-sudanesischer Mobilfunkunternehmer
Shararren dan kasuwar Sudan Mo IbrahimHoto: Hollie Adams/AFP/Getty Images

A nata banagaren Ingrid Hamma da ke zama guda daga cikin shugabannin kungiyar Global Perspective Initiave da ke taimakawa matan da rikici ya rutsa da su, na ganin nahiyar Afirka na kan habaka kuma duniya na gab da ganin Afirka yadda suka ga Asiya a shekaru 30 da suka gabata. A cewarta dole nahiyar Turai ta saka Afirka cikin manyan abubuwan da ta sanya a gaba, domin samun nasara a dangantakar nahiyoyin biyu.

Karin Bayani: Schulz yana da masaniya kan Afirka

A yayin da dama ke masu cike da fatan ganin wannan sabuwar dangantaka ta kullu, masanin dangantakar Turai da nahiyar Afirka Farfesa Robert Kappel da ke jami'ar birnin Leipzig na Jamus, na ganin dole sai Turai ta sauya yadda take kallon Afirka. A cewarsa, babu daidaito a dangantakar kasuwanci da ke tsakanin Afirkan da Turai. Ya kara da cewa dole kasashen EU su aminta cewa sun gaza taimakawa Afirka a wajen magance matsalar tsaro, a ganinsa kafin a kai ga cimma wata gajiya a fannin tatalin arzikin kasashen, dole sai an kawo karshen ayyukan ta'addanci.