Matatar Dangote za ta warware matsalolin man Najeriya?
September 5, 2024Bincike dai ya tabbatar da Gungun kanfanin na "Dangote Refinery" cewa ana dakon hukumomi su kayyade farashin man fetur din na Dangote kafin a sake shi ga jama'a. To sai dai wannan karin kudin mai na baya-bayan nan ya nuna cewa farashin kayan abinci da zirga-zirga ababan hawa sun sake tashin gwauran zabi inda a yanzu ake sayar da man fetur lita daya a Naira 897 maimakon Naira 568 a kowace lita a fadin kasar. Sai dai a daura da haka farashin man fetur din a arewacin kasar ya tasamma Naira dubu daya da dari biyu kan kowace lita.
Karin Bayani: Ko NNPC za ta kyale matatar Dangote?
Kasancewar muhimmancin Kungiyar IPMAN da ke da alhakin sayar da man fetur a kauyuka da birane ya sanya na tuntubi Alhaji Zannah Mustafa daya daga cikin shugabannin kungiyar a Nijeriya kan batun wannan kayyade farashi na man Dangote, inda yake cewa kamfanin mai na kasa kadai ka iya sayan kaya a wajen su kamar yarda suke saya a ketare ake kawo wa a raba wa 'yan kasuwa, su kuma su raba gidajen mai domin sayarwa ga jama'a. Yanzu dai a bisa bincike ya nuna cewwa matatar kanfanin mai na Dangote ta shirya tsaf inda take jiran kayyade farashin kowace lita ga 'an kasa.