Najeriya:Takaddamar Dangote da NNPC
July 22, 2024Aliko Dangoten dai, na tsakiyar wani sabon rikicin makamashi cikin kasar. A cikin babban fata ne Tarayyar Najeriyar ta yi nasarar kai wa ya zuwa samun matatar man fetur din, wadda ke iya cimma bukatar makamashin mai wahala. To sai dai kuma wata bakar siyasa ta gida, na barazana ga makomar matatar da jagoranta yake fadin tana a kasuwa. Dangote na tsakiyar wani rikici da gwamnatin ta Abuja, kuma ya nemi kamfanin man na NNPC ya sai matatar da ke iya tace ganga dubu 650 na hajar man kusan kullum. Ana shirin kai kololuwa cikin wani rikicin kudi da iko na kasar, bayan da Aliko Dangoten ya yi zargin cewa kamfanonin da ke aikin hakar mai a kasar, na hana shi damar sayen danyen man da matatar ke da bukata domin aikin nata.
Karin Bayani: An fara kai danyen mai zuwa matatar Dangote
Rikicin kuma da ya kalli gwamnatin kasar da zargin kamfanin na Dangoten da sai da hajja mara kyau, ko bayan neman babakere a cikin masana'antar da ke da tasiri ga tattalin arziki da siyasa. Dangoten dai ya nemi kamfanin mai na kasar NNPC ya saye hannun jarin attajirin, ya kuma karbi matatar ta zamo karkashin ikonsa. Kokarin babakere ko kuma neman ceto ga kasa dai, a ka'ida ta rubutu an tsara matatar Dangoten za ta tace litar man fetur miliyan 49 da ta Diseal miliyan 26 ko bayan man jirgi lita miliyan 12 cikin kasar da ke kashe dalar Amurka kusan miliyan 3000 a wata a kokarin biyan bukatar makamashi.
Duk da cewar dai Najeriyar ta dade tana zaman jiran kammala aiki na matatar, daga dukkan alamu an samu kuskure a bangaren Dangoten a tunanin Mohammed Lawal da ke zaman wani tsohon dan kwamitin gudanarwa na kamfanin man NNPC. A cewarsa NNPC ba za ta sai matatar ba domin ba ta da kudin, idan ma tana da kudin to ba za ta saya ba saboda dalilai na tattalin arzikin kasar. Kuma lokacin da zai gina matatar bai nemi shawarar NNPC ba, haka kawai ya tashi saboda yana da kudi yana da hanyoyi ya fara gini. Ba zai yi wu a ce duk wanda zai sa yi kananzir ko fetur sai ya je wurin Dangote ba, kamar yadda ya zamo zakara a harkar sumunti da sukari.
Karin Bayani: Karancin man fetur na kara tsanani a Najeriya
An dai dade ana kallon matatar da idanun tabbatar da dogaro da kai na Tarayyar Najeriyar cikin batun makamashi, ko bayan ceto tattalin arzikin kasar da ke tangal-tangal. Sabon rikicin kuma da a tunanin Dakta Isa Abdullahi da ke zaman kwararre ga tattalin arziki a Najeriyar, na zaman alamun karfin dillalan a fasa kowa ya rasa da ke tafi da harkokin makamashi cikin kasar a halin yanzu. Sabon rikicin na Dangote dai daga dukkan alamu na iya tasiri, ga kokarin gwamnatin kasar cikin farautar masu zuba jari na waje. Masu mulkin na Abuja dai, na dada dora fatan kasar na ci-gaba a jarin gina kamfanoni da samar da miliyoyin ayyuka ga matasan da ke zaman kashe wando