1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tinubu: Bukatar dawo da dimukuradiyya a Nijar

September 20, 2023

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce ya dukufa wajen sake amfani da dokoki da kundin tsarin mulki wajen magance matsalolin siyasa da na tattalin arziki da Nijar ke fuskanta bayan juyin mulkin soji

https://p.dw.com/p/4Wc5M
Shugaban Najeriyai Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriyai Bola Ahmed TinubuHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York na kasar Amurka,

Ya ce a shirye suke su aike da sojoji don mayar da Nijar kan turbar dimukuradiyya, matukar aka gaza cimma sulhu da sojojin.

Tun a watan Agustan da ya gabata ne dai gwamnatin mulkin sojin Nijar din ta umarci dakarunta da su zauna cikin shiri, bayan da ECOWAS ta yi barazanar aikewa da sojojinta don murkushe gwamnatin sojin da ta kira haramtacciya a Nijar.