1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: kiki-kaka kan mika mulki cikin hanzari

September 1, 2023

A dadai lokacin da tukun saka tsakanin jagororin sojan Nijar da Faransa ke kare kamari, sojojin sun yi gum da baki kan tayin da kasashen Aljeriya da Najeriya suka yi masu na mika mulki ga farar hula cikin hanzari.

https://p.dw.com/p/4Vqoi
Birgediya Janar Abdourahamane Tiani, jagoran mulkin sojan Nijar
Sojoji Nijar sun ki karbar tayin mika mulki a gajeren lokaciHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Yayin da Aljeriya ta bukaci sojojin da su gudanar da mulkin rikon kwarya na watanni shida karkashin jagorancin shugaba na farar hula, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya yi jirwaye mai kama wanka kan rikon kwarya na watanni tara kamar yadda sojoji da suka yi a Tarayyar Najeriya a shekararar 1999.

Karin bayani: ECOWAS: Sojojin Nijar su mika mulki cikin wata tara

To sai dai ba bu wata sanarwa daga majalisar sojojin karkashibn Birgediya Janar Abdourahane Tiani kan wadannan shawarwaru da makwabtan na Nijar suka bayar domin warware dambarwar da kasar ta fada.

Karin bayani: Sojojin Nijar: Ba za mu wuce shekaru uku ba

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta nemi ganawa da sojojin kan sanarwar da suka fidda ta dakatar da ayyukan kungiyoyin kasa da kasa a yankunan Nijar masu fama da matsalar tsaro.