Tinubu ya dakatar da tafiye-tafiyen jami'an gwamnati
March 21, 2024Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsara kashe Naira miliyan bakwai domin zırga- zirga zuwa kasashen waje, a yayın da mataimakinsa zai kashe miliyan dubu 1.2 kamar yadda kasafin kudin Najeriya na bana ya tanada. Sai dai a wata sabuwar sanarwa, fadar gwamnatin kasar ta dakatar da duk wata tafiya zuwa waje. Babban jami’i na fadar mulki Femi Gbajabiamila ya ambato bukatar rage kisan kudi don neman inganta tattalin arziki a cikin muhimman dalilan matakin da ke da niyyar aike sako.
Karin bayani: Najeriya: Illar yawan kudade a hannun Jama'a
Tun daga farkon watan Afrilu ne, shugaban kasar Najeriya ya umarci tsayar da zirga-zirgar har na tsawon watanni guda uku a karon farko, kuma duk wata tafiya ta wajibi na bukatar amincewa ta shugaban kasar akalla tsawon makonni biyu kafin yin ta. Sabon umarnin na kara fitowa fili da irin girman rashin kudin da ke cikin Najeriya a halin yanzu. Dr Isa Abdullahi da ke zama kwarrare a fannin tattalin arziki ya ce matakin ya yi daidai da kokarin ceto kasar daga cikin yanayi maras kyau.
Karin bayani: Soke izinin canji: neman gyara ko kassara sana'a?
A wani abin da ke zama ba sabun ba, matakin ya hada kan gwamnatin kasar da bangaren masu adawa. Ibrahim Abdullahi, mataimakin kakakin jam’iyyar PDP ta adawa ya ce shugaba Tinubu na shirin burge masu lema ta kasar in har ya kai ga aiwatar da sabon kudurin.
Karin bayani: Najeriya: Shirin inganta tattalin arziki
Sa ido cikin karatu na adawa ko kuma goyon baya ga kokarin ginin kasa, sannu a hankali masu mulkintarayyar Najeriya na kokawa ta neman hanyoyin sake dora daukacin kasar cikin karatun daidai, kuma sun dauki lokaci suna kokawa bisa rushewar tattalin arziki kasar. Sai dai a tunanin Comrade Saidu Bello da ke zama tsohon jami'i a hukumar tara haraji ta kasar, matakin hana tafiye-tafiye na masu mulki ya yi kadan, ya kuma makara a kokarin ceto lamura na tattalin arzikin da ke fadin jari hujja.