Najeriya za ta sayar da wasu kadarorinta
August 22, 2023Sama da kaso 95 cikin dari na kudaden da ke zuwa aljihun gwamnatin tarayyar Najeriya ya na tafiya ne wajen biyan kudin ruwa da ma bashin da ya kai wa kasar iya wuya a halin yanzu. Sai dai kuma sabbin mahukuntan Najeriyar sun ce suna shirin sayar da wasu kadarorin gwamnatin kasar da nufin tara Dalar Amurka miliyan dubu 17 domin gudanar da harkokin mulki.
Karin bayani
Shirin sayar da kadarorin gwamnatin Najeriya ya janyo cece-kuce
Kama daga masana'antun karafa ya zuwa matatun mai na kasar dai, tarrayar Najeriyar na kallon kadarori da yawa a wani abin da ke nuna girman rashin kudin da ke gaban masu mulkin kasar. Akalla kaddarori 70 ne dai ke cikin rajistar gwamnatin kasar da sunan ciniki a Najeriyar da ke da nauyin bashi. Dr Isa Abdullahi kwarrare kan tattalin arzikin Najeriyar ya ce sabuwar dabarar na iya taimaka wa masu mulkin kasar.
Kokarin yadda kwallon mangoro, ko kuma wasoso da dukiyar al'umma dai, an dauki lokaci ana ta siyasa mai zafi kan batun kadarorin. Kuma kama daga 'yan kodago zuwa ga 'yan adawa, an yi nisa cikin kace nace kan cinikin kadarorin.
Tsohuwar gwamnatin Yar Adu'a alal misali ta yi watsar da cinikin matatun mai na gwamnatin Chief Olusegun obasanjo bayan adawa mai zafi a cikin kasar.
Kokarin satar kudi, ko kuma cika alkawari ga 'yan kasa, ana kallon rage kashe kudi a bangaren masu mulki na iya kaiwa ga biyan bukata.