Najeriya: Tinubu zai wa APC takara
June 8, 2022Tsohon gwamnan jihar ta Lagos kana jigo a jam'iyyar ta APC mai mulki a Najeriyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben da gagrumin rinjaye. A yayin da tsohon ministan sufuri na kasar kana tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi ke biye masa da kuri'a 316. Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya zo na na uku a zaben na fidda gwani na jam'iyyar APC da kuri'u 235, yayin kuma da shugaban majalisar dattawan Najeriyar Sanata Ahmed Lawal ke zaman na hudu da kuri'u 152. Tuni dai bangaren Tinubun suka fara tsallen murnar nasarar da ke iya sauya da dama a cikin fagen siyasar Tarayyar Najeriyar. Tinubun dai, na da bukatar hada kan bangarorin APC da suka dauki lokaci suna dagun hakarkari da nunin yatsa a tsakanin juna.
An dai shiga shi kansa zaben ne kai a rabe kuma ana shirin fita a cikin karuwar rabuwar kai kama daga ta kabilanci da kila ma babancin addini, musammin a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar daga sashen Kudu maso Yammacin kasar ta kabilar ta Tinubu. To sai dai kuma a tunanin Faruk BB Faruk mai sharhi kan al'amuran siyasa a kasar, ana shirin ganin dabam a fagen siyasa sakamakon bullar Tinubun da ke takama da karfin dukiya da kuma masu fada ajin APC suka kasa hanawa ya zamo zakaran da ke bukatar cara. Koma dai ya take shirin kayawa a tsakanin masu tsintsiyar da ke neman dorawa kan mulki da abokan takunsu na lema dai, shi kansa shugaban kasar bai boye ba dangane da hada kai da nufin kai wa ya zuwa nasarar jam'iyyar da a cewarsa ta yi kokari a shekarun da ta kwashe tana mulki a kasar.