Jam'iyyar APC a Najeriya na cikin rudu
June 3, 2022Gwagwarmayar neman gado na shugaban kasar ne dai ke cikin tsakiyar rikicin da ke tafarfasa a halin yanzu, kuma ke neman farraka 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki. Tuni dai wasu a cikin manyan masu takarar ke zargin ana neman yi musu wakaci ka tashi, a kokarin fitar da dan takarar sulhu cikin jam'iyyar. To sai dai kuma kalaman jagoran jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu na cewar shi ne sanadin nasarar shugaban kasar a zaben na shekara ta 2015, ya janyo daga hakarkari a tsakanin magoya bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Karin Bayani: Siyasar kabilanci na son kunno kai a Najeriya
Alhaji Bashir Ibrahim Gwammaja dai, na zaman daya a cikin jagororin APC da kuma ya ce Tinubun na neman wuce gona cikin iri a kalaman nasa. Kokarin maimata rabon kudin 'yan lema ko kuma kai wa ya zuwa a fasa kowa ya rasa a siyasar dai, wani taro a tsakanin gwamnonin APC da shugaban kasar ya rushe bayan da mafi yawan gwamnonin sukai uwar watsi da gayyata zuwa fadar gwamnatin kasar. A wani abun da ke nuna irin girman rikici a tsakanin manyan 'ya'yan APC masu shirin zuwa babban taro. APC dai na rabe, a tsakanin magoya bayan Tinubun da ke fatan gwada kwanji a cikin babban taron da kuma masu neman jagoranci na shugaban kasar zuwa Gabas a siyasar ta masu tsintsiyar.
Mohammed Bello Shehu dai na zaman daya a cikin 'ya'ya na tsohuwar CPC da su ka kai ga hadewa wajen suka haifi APC, ya kuma ce Tinubun ya dade yana nadi yana saukewa kafin sabon tawayen da ke barazana ga makomar jam'iyyar mai mulkin Najeriya a halin yanzu. Sannu a hankali dai takarar APC na neman komawa ya zuwa takarar mutum hudu, wadanda suka hada shi kansa Tinubun da mataimakin shugaban kasar Osinbajo ko bayan tsohon ministan sufuri Rotimi Ameachi sannan kuma da shugaban majalisar dattawa na kasar Sanata Ahmed lawal.
Karin Bayani: Martani kan nasarar Atiku a zaben fid da gwani
Kwamitin da ya tantance masu takarar 23 dai, ya ce ya soke takarar mutane 10 da ba su cika ka'idar taka rawa a cikin zaben ba duk da kisan miliyoyin Nairori domin cika buri. To sai dai kuma ko bayan bangaren shugaban kasar, su kansu magoya bayan Osinbajon da ke neman gwada kwanjin na zargin jagoran APC da nuna alamun rudewa a siyasar da ke ta nuna alamun ko mutuwa ko yin rai. Jan aikin da ke gaban APC dai na zaman hadiye maitar mulki, tare da ceton APC mai nuna alamun tangal-tangal da kila kai karshen daurin tsintsiyar da ke shirin share takwas bisa mulki.