1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta sake dage shari'ar wa'adin karbar Naira

Uwais Abubakar Idris
February 22, 2023

Kotun kolin Najeriya da ta yi zama a karkashin jagorancin mai shari'a Okoro, ya saurari mahawarar da bangarori biyu a shari'ar suka tabka.

https://p.dw.com/p/4NrGk
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Kotun kolin Najeriya ta tsayar da ranar 3 ga watan Maris don yanke hukunci a kan  karar da gwamnoni 16 suka shigar na kalubalantar gwamnatin Najeriya a kan wa'adin da ta sanya na daina amfani da tsofaffin kudi da aka sauya wa fasali.

Karin bayani:Najeriya: Kalubalen sauya takardun Naira 

Kotun kolin Najeriyar dai ta ci gaba da sauraren wannan shari'a ne da alkalai bakwai na kotun ke yi a karkashin jagorancin mai shari'a John Okoro inda suka saurari muhawarar da bangarorin biyu a shari'ar suka yi a gaban kotu, watau bangaren gwamnonin Najeriyar da a yanzu suka kai 17 da suka ja daga da na gwamnatin Najeriyar watau gwamnan babban bankin kasar da kuma ministan shari'a. An dai tafka dogon turanci a kan wannan batu, musamman zargin kin bin umurnin kotu da gwamnatin Najeriyar ta yi. Chief Kanu Agabi shine ke jagorantar lauyoyin da ke kare gwamnatin Najeriyar.

Tsohuwar Naira
Tsohuwar NairaHoto: Getty Images

Ya ce "Shugaban Najeriya ba zai yi wani abu da zai raina iko da karfin doka na wannan kotu ba, duka muna kokari ne na shawo kan mawuyacin halin da muke ciki inda muke kenan, shugaban kasa kokarin da yake kenan ita ma kotun koli haka, lamari ne na kasa daya al'umma daya. Ni a sanina babu wasu bangarori a shari'ar nan, lamari daya ne na kasar nan, kuma muna kokari shawo kan matsalar nan ne''.

Karin bayani: Najeriya: Takaddama kan sauya fasalin kudi

Su dai gwamnonin suna son kotu ta tilastawa gwamnati ta yi watsi da tsarinta kudi bisa ga sabbin takardun kudin da aka bullo da su a kasar musamman wa'adin da ta sanya na daina amfani da kudin.  Sun dage kan cewa daukacin tsarin ya sabawa tsarin mulkin Najeriya domin shugaban kasa bai tuntubi sassan da suka dace ba, kuma wa'din daina karbar kudin ya saba dokar babban bankin Najeriya. Moyosore Onigbanjo shi ne Attorney janar na jihar Lagos wanda ke cikin lauyoyin da ke kare gwamnonin: 

Ya ce "Mun zo kotu ne domin samun sauki da saita sakamakon matsayin da wannan sabon tsari na kudi ya jefa al'ummarmu a ciki, don an kai ga tada fitina a dalilin wannan matsala a jihohi, duka saboda kin bin kai'da da matsaloli na wannan manufa ta gwamnatin Najeriya".

Kidayar tsohuwar Naira
Kidayar tsohuwar NairaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Tuni wasu gwamnoni suka bada umurnin a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin a jihohinsu abin da ake ganin sabawa umurnin shugaban Najeriyar ne. Mallam Nasiru El Rufai gwamnan jihar Kaduna ya ce babu dokar da suka saba.

Karin bayani:Rudani kan tsawaita wa'adin Naira a Najeriya 

Bayan sauraren dukkanin muhawara daga bangarorin biyu mai shari'a John Okoro ya tsayar da ranar 3 ga watan Maris mai zuwa domin yanke hukuncin a kan wannan shari'a da ‘yan Najeriya ke sa ido don ganin ko za'a dauki matakin da zai saukaka halin da suka shiga na karancin kudi da duk da alkawarin da babban bankin kasar ya yi har yanzu dai babu sabbin takardun kudin na Naira.