Kais Saied ya rusa majalisar zartaswa
July 26, 2021Shugaba Kais Saied ya sanar da rusa gwamnatin Firaminista Hichem Mechichi da majalisar dokokin kasar da jam'iyyar Ennahda ta masu kishin Islama ke da rinjaye a cikinta, gami da dagewa dukkanin 'yan majalisu da ministocin kasarkariyar da doka ta ba su. Shugaban ya dauki wannan matakin ne da nufin gudanar da bincike kan wadanda ake zargi da gazawa ko aikata laifuffukan da suka janwo tabarbarewar tattalin arziki da na kiwon lafiyar kasar, matakin da ya ce ya dauka domin ceto kasar da al'ummarta. Tuni dai rundunar sojojin kasar ta mamaye majalisar tare da hana duk wani dan majalisa shiga.
Karin Bayani: Tunusiya na zaman makokin rasuwar Essebsi
Kamar yadda suma daruruwan 'yan kasar suka bazu a kan tituna, domin nuna murnarsu da matakin da shugaban kasar ya dauka da suke ganin shi ne danbar sake dora kasar kan turba madadaidai ciya. Sai dai a hannu guda 'yan siyasar Tunusiyan na ganin wannan mataki da shugaban ya dauka tamkar juyin mulki, suna gargadin cewa shi kansa ya jira yaga abun da zai biyo baya. Moncef Marzouki tsohon shugaban kasar na Tunisiya ya ce masu farin cikin kawar da kungiyar Ennahda, su daina murna,domin karensu ne ya kama zaki. Tuni dai jam'iyyar Ennahda da ke da rinjaye a majalisar ta siffanta wannan matakin da juyin mulki, tana mai yin kira ga 'yan kasar da su fito su kalubalance shi.