Wani dan Afghanistan ya kashe mutane biyu a kudancin Jamus
January 22, 2025Wani 'dan asalin Afghanistan da ke zaune a nan Jamus ya far wa wasu mutane da wuka inda ya halaka mutum biyu ciki har da yaro karami 'dan shekara biyu a birnin Aschaffenburg da ke jihar Bavaria. 'Yan sandan yankin sun ce maharin ya jikkata wasu mutanen guda biyu inda suke ci gaba da karbar magani a asibiti.
Karin bayani:Harin Magdeburg zai zama maudi'i a yakin neman zaben Jamus?
'Yan sandan Bavaria sun cafke mutumin da ake zargi da kai harin, lamarin na daya daga cikin barazanar da Jamus take fuskanta na kai hare-haren kan mai uwa da wabi da wuka a watannin baya bayan nan. Hukumomin tsaron yankin da ke kudancin Jamus na ci gaba da bincike kan harin duk da cewa ba su bayyana makasudin kai farmakin ba.
Karin bayani: Ana bincike kan barazanar sake kai hari a Jamus
Harin na zuwa ne gabanin zaben wuri da za a gudanar a Jamus a ranar 23 ga watan Fabrairu, inda kawancen jam'iyyun CDU/CSU ke kan gaba da kashi 30 cikin 100 a kuri'ar jin ra'ayin mutane da aka gudanar, yayin da jam'iyyar AfD mai ra'yin kyamar baki ke bi mata da kashi 20, sai kuma jam'iyyar SPD ta shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ke a matsayi na uku.