Yaki da fataucin dan adam
August 1, 2021Ranar 30 ga watan Yulin kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don yaki da safarar mutane musamman kananan yara. Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwa matsalar yin safarar mutane musamman kanana yara da masu wannan dabi'a suka sauya salo dabam daga wadanda aka sani. Ana alakanta talaucin da kuma neman kyakyawar makoma ko kwadayin tara abin duniya a matsayin dalilan da ke saka yin fataucin mutane zuwa wasu garuruwa ko ma kasashe inda a karshe ba a iya ma cimma burin da ake nema.
Karin Bayani: Tunawa da cinikin bayi
Wannan matsala ta fataucin mutane ya zama ruwan dare gama duniya a Najeriya, kuma ba babba ba yaro kuma ba ga mai lafiya kawai ba har da masu fama da lalura ta musamman. A yayin da hukumomi ke toshe kafofi da hanyoyin na yin fataucin bani adama, masu wannan sana'ar suna fito da sabbin dabaru na yadda za su kwashi mutane zuwa wuraren da za su kai don yin aikatau ko kuma wasu abubuwa na neman kudi halattatu ko kuma akasin haka.
Karin Bayani: Yaki da bauta a duniya
Rahotanni sun nuna cewa, akwai mutane musamman mata da ke zuwa shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya inda suke yin hayar yara domin zuwa wasu garuruwa da su da nufin yin bara, su kan nuna cewa marayu ne, a taimaka musu amma daga baya a biya iyayen su. Masu fama da lalura ta musamman, sune wannan matsala ta fi shafa kamar yadda Kwamred Muhammad Abba Isa shugaban Kungiyar masu fama da lalura ta musamman a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya ya fadi.
Karin Bayani: Badakalar safarar kananan yara
Yayin da ake ci gaba da laluben hanyoyin da za a dakile wannan matsala. Ita kuwa Hukumar kula da masu kaura ta Majalisar Dinkin Duniya, ta nuna cewa masu safarar mutane daga Najeriya sun mayar da kasar Mali a matsayin wurin da su ka fi samun nasarar kai mutane da suka yi safarar su.