1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun sake kashe wani basarake a Najeriya

October 9, 2024

Mai rike da sarautar Mai Babashehu Mai Musinema a jihar Borno na daga cikin wadanda mayakan Boko Haram suka halaka da wasu sojoji a kwanton bauna da suka kai a karamar hukumar Marte da ke jihar Bornon Najeriya.

https://p.dw.com/p/4laOZ
Jihar Borno ta Najeriya ta shafe shekaru a yanayi na rashin cikakken tsaro
Jihar Borno ta Najeriya ta shafe shekaru a yanayi na rashin cikakken tsaroHoto: .

Mayakan Boko Haram sun bude wuta ne kan ayarin basaraken da yake samun rakiyar sojoji da dakarun sa kai na  JTf a kan hanyarsu ta zuwa duba hanyar da ta lallace a tsakanin Marte da Dikwa domin gyarawa. Daga cikin wadanda wannan harin kwanton bauna ya ritsa da su har da basarake Mai Babashehu Mai Musinema da Sojoji biyu gami da Kwamnadojin matasan Civilian JTF na karamar hukumar Marte. Sanna akwai mutane da dama da suka samu munanan raunuka da aka kai Maiduguri don duba lafiyarsu.

Marte na nusa alhini bayan kashe basarake

Baana Hussaini Marte  da ya tsira daga wannan hari ya ce: "Shugaban civilian JTF da yaransa guda biyu da hakimin Musinema da kimanin mutane biyar ,duk ‘yan Boko Haram sun bude musu wuta kuma dukkansu sun mutu." Amma a lokacin da yake bayani kan hali da ake ciki a Marte, sai Baana Hussani Marte ya ce: "Mutane na cikin fargaba yanzu haka bayan da suka samu tsinkewar zuciya, amma jami’an tsaron na Marte bayan da hankalin mutane ya tashi.”

Karin bayani:Ta'addanci ya ta'azzara a Najeriya

Jama'a na rasa muhallinsu a jihar Borno bayan hare-haren 'yan bindiga
Jama'a na rasa muhallinsu a jihar Borno bayan hare-haren 'yan bindigaHoto: Jossy Ola/AP Photo/picture alliance

Mayakan Boko haram sun farfado da sabbin hare-hare, abin da ke kara jefa al’umma cikin fargabar komawa halin da suka shiga a baya. Ko a karshen makon, mayakan sun kai wani hari a garin Gaidam inda suka halaka mutum daya tare da lalata Kabarin Shehu Muhammadu Ainoma da ke zama mashahurin malami na garin. Wannan ne ma ya sa Bashir Gudumbali ya bayyana damuwa kan yanayin tsaro na wannan shiyya, inda ya ce: "Akwai wasu sassa da ake fuskantar sace-sacen al’umma domin a nemi kudin fansa, sannan wani bangare na ‘yan ta’adda na Boko Haram suna fitowa suna kai hare-hare a jihar Borno.”

Bukatar tsaurara matakan tsaro a sassa jihar Borno

Sai dai Farfesa Lawal Jafar Tahir na jami’ar jihar Yobe da ke Damaturu ya cewa dole a kara kaimi idan ana son magance matsalar tsaro. Ya ce:  "Wannnan yaki ba a kare shi ba, akwai  bukatar sake daure damtse domin a tabbatar da cewa an magance wannan matsalar. Ammam har yanzu gaskiya akwai matsala sosai dangane da sha’anin tsaro.."

Karin bayani:Dabi'ar sace-sacen mutane na kara kamari a Najeriya

Gwamnan Borno Babagana Zulum na neman hadin kan al'umma wajen yakar ta'addanci
Gwamnan Borno Babagana Zulum na neman hadin kan al'umma wajen yakar ta'addanciHoto: Mohamed Tidjani Hassane/DW

Wannan hari na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi zargin cewa mayakan Boko Haram na buya a cikin sansanonin ‘yan gudun hijira domin samun mafaka bayan aikata ta’addanci. Gwamnan ya ce: "Wasu daga cikin mayakan Boko Haram suna kwana a cikin sansanin ‘yan gudun hijira, sai da sassafe su fita su koma maboyarsu. Wannan ba abu ne da za mu yarda da shi ba. Muna shawartar al’umma da sukai rahotannin dukanin bata gari da laifuka da ake aikatawa a wadannan wurare zuwa wajen Sojoji da sauran jami’an tsaro domin a dauki matakai da suka kamata.....”

Sojojin Najeriya  na cewa suna bakin kokarinsu wajen magance wadannan hare-hare a jihar Borno, amma suna nemane jama’a su ba da gudumowa domin a iya magance matsalar tsaro da ake fuskanta a sassan kasar.