Fatan 'yan Najeriya ga zaben Amirka
November 3, 2020Duk da dimbin nisan da ke a tsakani dai, zaben na kasar Amirka na ci gaba da tasiri a tsakanin miliyoyin al'ummar Tarayyar Najeriyar da ke masa kallon tsaf. Kuma hankali ya rabu tsakanin 'yan goyon bayan shugaba mai ci Donald Trump da kuma Joe Biden da ke kokari na kwace goruba a hannun kuturu. Kama daga 'yan ra'ayi na rikau ya zuwa ga masu neman sauyin na Amirka dai, daukaci na masu siyasar ta Amirka dai, sun dauki lokaci suna tsomin baki a cikin harkokin kasashe irinsu Najeriya, tare da tasiri a tunanin 'yan boko d ragowa na shugabanni na kasar.
Karin Bayani: Jawabin Trump na farko ga majalisa
Alal ga misali dai an ruwaito shugaban Amirka da ke kai yanzu, na kiran kasashe irin Najeriyar a matsayin kasashe marasa kyau da al'ummarsu ke rayuwa a cikin kunci, baya ga dakile izinin zama cikin kasar ga al'ummar Najeriyar da ke fatan zama a cikin Amirka.
Ya zuwa yanzu ma dai Amirkan na zaman kasa daya tilo, da ta sa kafa ta shure zaben tsohuwar ministan kudi ta tarrayar Najeriyar Ngozi Oknojo-Iweala a matsayin shugabar kungiyar ciniki ta duniya WTO. Farfesa Sadiq Abba dai na zaman masanin harkokin kasa da kasa a jami'ar babban birnin Tarayya ta Abuja, da kuma ya ce duk da matsayin na Trump akwai alamun adalci a cikin manufar ta Amirka, ga kasashe irin su Najeriya a karkashin mulkinsa. Yaki da masu zambar mulki, ko kuma kokarin wulakanta kasa dai, in har wasu na kallon Biden da kasa taimakawa Najeriyar da ma kasashen Afirka dai, a tunanin Dakta Umar Ardo da ke kallon 'yan sauyin na zaman abokan al'adar Tarayyar Najeriya na gadon gado.
Karin Bayani: Zaben Amirka: Wacece Kamala Harris?
To sai dai kuma in har 'yan sauyin sun taka rawa a cikin yakin 'yancin, a fadar Faruk BB Faruk masu neman sauyin sun taka sun zubar a idanun Najeriyar, sakamkon kin sayar mata da makamai domin yaki da ta'adda. To sai dai ko ta ina yawun yake shirin ya zuba dai, Najeriyar na fatan samun karin fada aji a birnin na Washington, ko ba komai a wakilci na bakaken fata na duniya.