1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Najeriya ta kara albashin 'yan sanda

December 16, 2021

A wani mataki da gwamnatin kasar ta kira cika alkawarin da ke tsakaninta da 'yan kungiyar Endsars da suka yi zanga-zanga, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana karin albashi ga jami'an 'yan sanda na kasar.

https://p.dw.com/p/44Mlk
Nigeria Lagos | EndSars Demonstration
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Matasan da suka yamutse hazo dai sun ce rashin albashi mai inganci da kuma rashin kyawun aiki na zaman na kan gaba cikin hujjojjin cin zarafin da ake zargin 'yan sandan da aikatawa a kasar.

Kuma ko bayan rushe rundunar dai mahukuntan Abuja sun sha alwashin inganta aikin 'yan sandan da nufin kai karshen cin zarafin da ya dauki hankalin 'yan Najeriya. Alkawarin kuma da Abuja ta ce tana shirin ta cika da wani sabon karin albashi ga rundunar 'yan sandan.

Karin Bayani: Najeriya: Human Rights Watch ta ce gaskiya ta yi halinta a rahoton kisan EndSars

Kowane cikin 'yan sandan dai kuma daga farko na shekarar badi ta 2022 na shirin samun akalla kari na kaso 20 cikin 100 na albashi da alawus dinsa. Maigari Dingyadi dai na zaman ministan 'yan sanda na kasar da kuma ya ce matakin na da burin cika alkawarin da ke tsakanin gwamnatin kasar da matasan EndSARS.

Nigeria Lagos | EndSars Demonstration
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Wannan ne dai karo na farkon fari da jami'an 'yan sandan ke shirin dandana dadi na  zumar a cikin aikin da kimarsa ke kara shiga laka a idanu na 'yan kasar a halin yanzu. Kuma in har Abuja na neman burge masu tada kayar bayan a sabo na matakin dai daga duk alamu suna da babban aiki, a fadar Auwal Musa rafsanjani da ya taka rawa a jeri na zanga-zangar kai karshen SARS.

Kitso da kwarkwata cikin hali na tsaro, ko kuma neman inganta aiki dai ga su kansu jami'an 'yan sandan daga dukk alamu sabon karin na ya yi kadan yai tsaroro a fadar ACP Aliyu Alhassan da ke zaman wani tsohon dan sanda a kasar. Ana dai ta'allaka karuwar rashin tsaron Najeriya da rushewar aikin dan sandan da kundin tsarin mulki na kasar ya dorawa alhakin tabbatar da tsaron cikin gida, amma kuma ya rikide zuwa bara da cin zarafin al'umma.