SiyasaAsiya
'Yan sanda sun murkushe masu bore a Santanbul da Paris
May 1, 2024Talla
Dubun dubatar mutane sun fantsama kan tituna a sassa daban-daban na duniya domin gudanar da zanga-zangar adawa da yadda ake tafiyar da al'amuran da suka shafi rayuwar ma'aitaka.
Karin bayani: An tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Gaza a Turkiyya
Baya ga cafke mutane sama da 210 a dandalin Taksim na birnin Santanbul, 'yan sandan birnin Paris na kasar Faransa sun cafke mutane 25 a ke gudanar da boren karancin albashi da kuma bukatar dakatar da yakin Gaza.
Karin bayani: 'Yan kabilar Uighur na zanga-zanga a Turkiyya
A nan Jamus mutane 10 ne suka samu raunuka sakamakon arangama da sukayi a lokacin rangadin ranar ma'aikata a birnin Freiburg da ke kudu maso yammacin kasar ta Jamus.