1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman sasanta rikicin Siriya ya wargaje

Salissou BoukariFebruary 4, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da dakatar da tattaunawar da ake yi wajan sasanta rikicin siriya, inda ta sake tsayar da ranar 25 ga watan Febrairu Domin sake zama.

https://p.dw.com/p/1Hpjp
Hoto: Reuters/D. Balibouse

Batun tattaunawar sasanta rikicin Siriya da aka fara karshen mako dai ya ci tura, inda manzon Majalisar Dinkin Duniya Staffan de Mistura ya sanar da katse zaman da ake yi, a wani abun da ya kira karamin hutu. Da ma dai tun fara taron akasarin mutane sun nuna shakku kan makomomar sa inda suke ganin bai zai haifar da wani da mai ido ba, musamman ganin yadda yan tawaye suka dauki kwanaki gabanin fara taro kafin su isa birnin Jiniva, inda suka yi ta kai-kawo a kasar Saudiyya don amincewa da ainihin wadanda za su zama wakilai a wurin tattaunawar, sannan kuma ga batun zargin dakarun gwamnatin ta Siriya masu samun goyon bayan Rasha wajan kan ci gaba da kai hare-hare a yankunan da ke hannun 'yan tawayan.