Tunusiya: Nuna adawa ga shugaban kasa
September 27, 2021Zanga-zangar dai na zuwa ne, a daidai lokacin da babbar jam'iyyar adawar kasar Ennahda mai ra'ayin Islama ke daddarewa, inda manyan jami'anta 113 suka fice kan zargin rashin kyakkyawan jagoranci. Dandazon masu wannan zanga-zangar da a tsakiyar birnin na Tunis sun keta shingayen jami'an tsaron da ke kokarin dakile su, kana suka fantsama kan titunan birnin suna rera taken nuna kyama ga shugaban kasar Kais Saied. Wasu kuwa cewa suke, bayan matakan tattarawa kansa iko da fatali da kundin tsarin mulki da Shugaba Saied din ya yi, ba shi da halaccin mulkin kasar balantana ma ace za a shiga tattaunawa da shi.
Wannan zanga-zangar dai ita ce mafi girma tun lokacin da Shugaba Saied ya kori firaministansa ya kuma dakatar da majalisar dokokin kasar a ranar 25 ga Yuli, kafin daga bisani ya nada kansa a matsayin babban mai gabatar da kara, lamarin da ya mayar da shi shugaba mai tattara iko a duniya. Kimanin kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa da na Tunisiya 20 ne suka yi tir da matakin nasa. A hannu guda, magoya bayan Shugaba Saied suma sun shirya tasu zanga-zangar domin nuna amincewarsu da matakan da ya dauka da suke siffantawa da na ceton kasa. Wasu kuwa kira suke da a yi garanbawul ga kundin tsarin mulkin kasar baki da ya. Masharhanta dai na nuna fargabar cewa, rashin shawo kan wannan matsala, ka iya jefa kasar cikin tsaka mai wuya.