SiyasaTurai
Ukraine ta bukaci karin taimako daga Birtaniya
July 19, 2024Talla
A wannan Jumma'a Shugaba Volodymyr Zelenskiy na kasar Ukraine ya gabatar da jawabi ga majalisar ministocin kasar Birtaniya karkashin sabon Firaminista Keir Starmer, game da matsayin Birtaniya na ci gaba da taimakon Ukraine kan kutsen da take fuskanta daga Rasha.
Karin Bayani: Sabon firaminista ya yi alkawarin sake gina kasar
Shugaban na Ukraine ya samu gagarumar tarba daga majalisar ministocin ya kuma jaddada kiran da yake yi wa kasashen Yammacin Duniya na amince da amfani da makamansu wajen kai harin ramuwa cikin Rasha. Ita dai Biratniya ta kasance sahun gaba na masu goyon bayan Ukraine tun lokacin da ta fuskanci kutse daga Rasha a shekara ta 2022.