1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rayuwar Merkel bayan mulkin shekaru 16

Sabine Kinkartz ARH/LMJ
December 1, 2021

Bayan tsawon shekaru 16 tana mulki, Angela Merkel za ta koma yin rayuwa bayan mulki. Mai shekaru 67 a duniya, ko yaya za ta tafiyar da rayuwarta ta gaba? Shin za ta yi wani abin ko kuma za ta yi rayuwarta a gida?

https://p.dw.com/p/43i8Q
Deutschland Bundeskanzlerin Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na shirin yin bankwana da mulkiHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Angela Merkel na sha'awar yin girke-girke musamman na gargajiya na Jamus wanda ba ta samu damar yin hakan ba a tsawon lokaci saboda aikinta na shugabanci, har bayan zabe kamar ga al'ada yadda ake yi a Jamus ta ci gaba da jagoranci kafin mika mulki ga sabon shugaba. Kadan ya rage Merkel din ta kamo kwanakin mulkin tsohon ubangidata wato Helmut Kohl. A makwannin baya-baya nan ta kasance tana ganawa da hukumomi na kasashe dabam-dabam domin yin bankwana. A cikin watan Yulin da ya gabata da ta kai ziyara Amirka inda aka karramata, ta ce ba ta da niyyar yin komai bayan ta sauka daga mukin. Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus din za ta yi rayuwarta a gidansu da suka yi wa gyara na hutu tare da maigidanta da ke Brandenburg. Ba dai za ta taba samun wata fargaba ba a kan sha'anin kudin shiga, a matsayinta na tsohuwar shugabr gwamnati.

Karin Bayani: Zaben 'yan majalisar dokoki na Tarayyar Jamus ya bar baya da kura

Duk da cewar a matsayin shugabar gwamnati kafin saukarta, abin da ake biyanta a wata shi ne Euro dubu 25 da kuma kudin alawus da ake ba ta a  matsayinta na mamba a majalisar dokoki na Euro dubu 10. Bayan ta sauka daga mulkin za a rika biyanta albashinta a tsawon watannin uku, sannan a tsawon watannin 21 za a rika biyan ta rabin abin a ake ba ta wanda a taikaice za ta samu kusan Euro 15000 kenan a wata. Kana za a ba ta jami'an tsaron da za su kula da kare lafiyarta da motar shiga da ofishi a cikin harabar majalisar dokoki, inda za ta samu masu taimakamata ma'aikata kamar guda shida da direbobi biyu har karshen rayuwarta.

BIldkombo Deutsche Bundeskanzler
Angela Merkel na shirin shiga rukunin tsofaffin shugabannin gwamnatin JamusHoto: AP Photo/picture alliance

Wasu dai daga cikin tsofaffin shugabannin gwamnati na Jamus da suka sauka da mulki, sun gudanar da ayyuka na cibiyoyin kamar su Helmut Kohl da Gehard Schröder. Ga misali Helmut Kohl ya kafa wata cibiyar da ke bayar da shawarwari a kan harkokin siyasa, wanda ya samu nasara a kai. Sai dai ko Angela Merkel na da irin wanna ra'ayi?: "Ina tsammnin zan kasance a gida, na yi tunanin tukuna na ga abin da yakamata na yi. Amma dai mai shekaru 67 a duniya, lokacin kadan ne da shi. Zan rika yin karance-karance da barci, zan dai ga abin da zan rika yi."

Karin Bayani: Merkel na ziyarar yankunan da ambaliyar ruwa ta afkawa

Babu dai tabbas yazuwa yanzu ko tsohuwar shugabar gwamnatin ta Jamus, za ta amince ta karbi wani matsayi na karramawa da ake bai wa tsofaffin shugabanin ko kuma aiki a karkashin cibiyar da za ta samar. Bisa ga dukkan alamu dai, za ta yi rayuwarta da mijinta Jochim Sauer masanin kimiyya malami a jam'iyyar Humboldt ta birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus din.