1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD na son a gaggauta kai agaji a Gaza

Abdourahamane Hassane
October 20, 2023

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi kira da a samar da agajin gaggawa ga al'ummar yankin Zirin Gaza, wanda Isra'ila ta rufe.

https://p.dw.com/p/4Xnz6
Hoto: Belal Khaled/AA/picture alliance

Gutteres ya bayyana a dandalin Twittercewar akwai bukatar kai agajin na abinci da ruwan sha da magunguna da kuma man fetur. A halin yanzu Guterres yana a Masar don tattaunawa da gwamnati game da bude iyakarRafah zuwa zirin Gaza. Ana kallon Rafah da cewar ita ce hanya daya tilo ta kawo kayan agaji a yankin na zirin Gaza. A ranar Alhamis din da ta gabata,an jibge manyan motoci sama da 160 dauke da kayayyakin jin kai a bangaren Masara gaban mashigar yankin zirin Gazan wanda aka shirya soma fara shigar da kasyan a ranar Asabar(21.10.23).