Najeriya: 'Yanci ga kananan hukumomi
May 24, 2022Wannan hukunci da kotu ta yi dai, ya nuna yadda aka rangada gwamnoni da kasa a gaban kotu a kan wannan bukata tasu na su ci gaba da kankame lalitar kanana hukumomin suna yadda suka so da ita a karkashin asusun hadin gwiwa tsakanin jihohin da kanana hukumomin. An dai jima ana zargin gwamnonin jihohin da yi wa kananan hukumomin kwange irin na kashin dankali, wato babba a sama ya danne kanana. Karkashin tsarin da kotun ta amince a yanzu dai, ya zama tilas kuma wajibi da zarara an raba kudin to a aika da su gaba daya zuwa asusun kananan hukumomin. Haka kuma ba a yarda kananan hukumomin su aika da kudin da suka zarce rabin miliyan zuwa wani asusun ba, domin gudun a bayar da hannun dama a karbe da na hagu daga gwamnonin da ke zama tamkar wani zaki ga shugabannin kananan hukumomin. A baya dai an zargi gwamnonin da yin waka ci wa tashi da kudin kananan hukumomin Najeriyar, musamman ta hanyar asusun na hadin gwiwa tsakaninsu. Tuni hukumar sa ido a kan bayanan sirri kan ta'ammuli da kudi ta Najeriyar, ta yi murna da wannan hukunci tare da gargadin cewa za ta saka ido sosai a kan yadda za a tafiyar da kudin kananan hukumomin kuma duk wanda ya saba za ta sanar da Hukumar Yaki da Almundahana da Kudin Jama'a ta kasar wato EFCC.