Baraka a cikin jam'iyyar PDP a Najeriya
April 9, 2024Bayan kwashe lokaci mai tsawo ana nuku-nuku a kan halin da jam'iyyar ta PDP ke ciki a Najeriyar, inda wasu daga cikin magoya bayanta suka shiga guna-gunin na nuna rashin gamsuwa da halin da jam'iyyar ta shiga ne, wadannan ‘yan jam'iyyar PDP su 60 da ke majalisar wakilan Najeriyar suka yi ta maza tare da yin barazana a kan lallai sai shugaban riko na jam'iyyar ya sauka daga mukamminsa, ko kum a jam'iyyar ta yi asarasu a matsayinsu na ‘yayanta, abin da zai iya karawa jam'iyya mai mulki karfi a majalisa.
Dalilan da 'yan siyasar na PDP suka bayyana a kan ficewa daga jam'iyyar
Sun nuna rashin jin dadinsu ne a kan yadda ake tafiyar da jam'iyyar wacce sannu a hankalin karsashinta ke raguwa a fagen siyasar Najeriyar, lamarin da ya kara muni tun bayan faduwa zaben da ta yi a babban zaben shugaban Najeriya. Shugaban jam'iyyar PDP na riko ambasada Umar Iliya Damagum ya karbi shugabancin jam'iyyar ce a yanayin na rikici wanda tun 2022 ya samo asali, ana masa zargin yana hulda da minstan Abuja Nyesom Wike wanda duk da dan jam'iyyar ce amma yake yiwa ASPC aiki.
Matsayin 'yan adawa a cikin tafiyar da harkokin gwamnati
Tuni masana a fanin kimiyyar siyasa a Najeriya irin su Farfesa Abubakar Umar Kari ke bayyana yadda aka yi jam'iyyar ta sake shiga wannan hali da hatsarin da ke fusknatarta a yanzu. Adawa a siyasa dai ita ce gishin demokurdiyya wanda rashinta ke haifar da matsaloli sosai. Da alamun wannan rikici farkonsa aka gani sanin cewa shugabancin jam'iyyun siyasa a Najeriya ya gaji rikici da yawan tsige shugabaninsu kama daga jam'iyyar da ke mulki zuwa ga jam'iyyun 'yan adawa.